Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Ayarin Motoci na farko na kayan agaji da mutanen Pakistan suka aike zuwa ga al'ummar Iran masu jarumtaka da tsayin daka, ya isa kasar. Wannan ayarin yana dauke da magunguna masu muhimmanci, kayan aikin likita, da kayayyakin tiyata, wadanda aka shirya kuma aka aika a matsayin wani bangare na kokarin tallafin jin kai domin tallafawa mabukata da wadanda abin ya shafa.
A cewar rahoton, wannan taimakon an tattara shi ne a karkashin kulawar Hujjatul-Islam wal-Muslimeen Sayyid Sajid Ali Naqavi, shugaban Majalisar Malaman Shi'a ta Pakistan, tare da hadin gwiwar Cibiyar Zahra (AS) da ke Karachi. Jama'ar Pakistan, masu ba da taimako, da cibiyoyin addini sun nuna hadin kai da goyon baya ga gwamnatin Musulunci ta Iran ta hanyar shiga cikin wannan himma.
Bayan isa Iran, wasu malamai daga Makarantar Hauza ta Qom sun karbi wannan Ayarin. An yanke shawarar cewa za a mika kayayyakin agaji ga kungiyar agaji ta Red Crescent ta Tehran da jami'ai masu kula da harkokin, domin a raba su ga cibiyoyin kiwon lafiya da mabukata cikin gaggawa. Jami'an da suka halarci taron tarbar sun dauki wannan mataki a matsayin alama ce ta hadin kai, tausayawa, da zumunci mai zurfi tsakanin kasashen Musulmi.
Your Comment